IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Shadar Imam Sadiq (AS) A London

15:08 - September 23, 2010
Lambar Labari: 1999934
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zama kan shahadar Imam Sadiq (AS) a birnin London na kasar Birtaniya, wanda cibiyar bunkasa harkokin Musulunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani bayani daga shafin sadarwa na yanr gizo na ic-el cewa, za a gudanar da wani zama kan shahadar Imam Sadiq (AS) a birnin London na kasar Birtaniya, wanda cibiyar bunkasa harkokin Musulunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin.

A yayin gudanar da wannan zaman taro mai albarka za a gabatar da jawabai da suka danganci rayuwarsa da kuma yadda taka gagarumar rawa wajen isar da sakon Allah ta hanyoyi daban-daban, ya kafa babbar cibiyar da har kasa ta nade al'ummar duniya ba za gushe suna amfana da ita ba.

Imam Sadiq (AS) ya shahara wajen yada ilimin addinin muslunci, wanda dukkanin bangarorin musulmi suka amfana da iliminsa mai albarka, kamar yadda ya sha wahala a hannun azzaluman sarakuna na wancan lokacin har zuwa shahdarsa.

660450



captcha