IQNA

An Bude Shafin Mayar Da Martani Kan Bakanta Sunan Musulunci

15:08 - September 23, 2010
Lambar Labari: 1999936
Bangaren kasa da kasa; An bude wani sabon shafin yanar gizo na musulmi, domin mayar da martani kan dukkanin ayyukan batunci da ake yi kan addinin muslunci da musulmi a duniya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na prnews cewa, An bude wani sabon shafin yanar gizo na musulmi, domin mayar da martani kan dukkanin ayyukan batunci da ake yi kan addinin muslunci da musulmi a duniya musamamn ma a kasashen turai.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan sabon shafin yanar gizo mai suna (muslim response.com) zai rika duba dukkanin abubuwan da ake dangantawa da Musulunci na batunci tare da mayar da martani kansu.

Haka nan kuma shafin zai rika kawo bayanai dangane da koyarwar addinin Musulunci ta hakika sabanin abin da makiyansa suke yadawa a duniya da nufin dushe haskensa.

660563



captcha