Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar kur'ani mai tsarki ta kasar Afirka ta kudu za ta sanar da shirye-shiryen gasar kur'ani mai tsarki ta share fage da za a gudanar a kasar, kuma za a sanar da sunayen wadanda suka cancanci shiga wannan gasa a cikin wannan mako.
Bayanin ya ci gaba da cewa, cibiyar kula da harkokin kur'ani mai tsarki ta kasar Afirka ta kudu ita ce za ta dauki nauyin shirya gudanar da wannan gasa a kasar, wadda za ta samu halartar makaranta da mahardata.
Wannan gasa dai a matsayin share fage ne za a gudanar da ita, inda ake sa ran gudanar da wata gagarumar gasar kur'ani a kasar a nan gaba, da za ta hada da wasu 'yan kasashen waje.
660720