Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin shafin yanar gizo na noelebanon an bayyana cewa, Jakadan jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Labanan ya jaddada wajabcin kare littafan da aka safkar daga sama musamamn ma kur'ani mai tsarki da a halin yanzu ake keta alfarmarsa a wasu kasashe.
Ghazamfar Roknabadi yabayyana hakan ne a a wani taro da kungiyar muslunci ta Amal Islami ta shirya a birnin Beirut, inda ya gabatar da jawabi a gaban mahalrta taron, da suka hada da malamai da kuma wasu fitattun 'yan siyasar kasar.
A cikin jawabanin nasa jakadan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada wajabcin tsayawa tare da duk wasu wadanda ake zalunta ako'ina cikin fadin duniya.
Haka nan kuma ya yi kakkausar kan kasashen yammacin turai da suke bayar da kafa wajen cin zarafin musulmi da abubuwan da suke girmamawa.
660604