IQNA

Iran Na Ganin Hadin Kan Kasashen Musulmi Zai Amnfanar Da Al'ummominsu

15:09 - September 23, 2010
Lambar Labari: 1999941
Bangaren siyasa; Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewa jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi amannar cewa hadin kai tsakanin gwamnatocn kasashen musulmi zai amfanar da dukaknin al'ummar musulmi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin shugaban kasa an bayyana cewa, shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad ya bayyana cewa jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi amannar cewa hadin kai tsakanin gwamnatocn kasashen musulmi zai amfanar da dukaknin al'ummar musulmi baki daya.

Ahmadinejad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Amr Musa a gefen babban taron majalisar dinkin duniya da ke gudana a birnin New York na kasar Amurka.

A bangare guda kuma sun tabo muhimman batutuwa da suke ci ma al'ummar musulmi tuwo a kwarya, musamman ma batun palastinu da ci gaba da aiwatar da syasar zalunci da mamaya da haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi.

660533



captcha