Bangaren kasa da kasa; Kura'ni mai tsarki shi ne babban taken taron bude masallatan kasar Jamus a wannan shekara, tare da bayyana shi a matsayin littafin da ya yi shekaru 1400 ba tare da samun canji ba.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar iqtisadiyya ta kasar Saudiyya an habarta cewa, kura'ni mai tsarki shi ne babban taken taron bude masallatan kasar Jamus a wannan shekara, tare da bayyana shi a matsayin littafin da ya yi shekaru 1400 ba tare da samun canji ba a cikinsa.
Bayanin ya ci gaba da cewa ana gudanar da wannan taro ne a daidai ranar da Jamus ta yamma ta hade da Jamus ta gabas, inda mabiya addinin Musulunci su ma sukan gudanar da nasu taruka a wannan ranar domin samun hadin kai tsakaninsu da sauran mabiya addinai na kasar.
Musulmi sukan yi amfani da wannan damar wajen shirya taruka, inda suke gayyatar wasu mabiya addinai musamman ma kiristoci domin su halarci taron nasu, domin samun masanaiya kan matsayin addinin Musulunci dangane da abubuwa da dama.
661542