IQNA

Za A Bude Ajujuwan Koyar Da Limaman Jamusu Harshen Kasar

15:46 - September 25, 2010
Lambar Labari: 2000958
Bangaren kasa da kasa; Za a bude wasu ajujuwa na koyar da malaman addini musamamn limamamn masallatan Juma'a akasar harshen jamusanci, da nufin samun damar cudanya da sauran al'ummar kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dilalncin labaran jihan na kasar Turkiya cewa, za a bude wasu ajujuwa na koyar da malaman addini musamamn limamamn masallatan Juma'a akasar harshen jamusanci, da nufin samun damar cudanya da sauran mutane.

An fara aiwatar da irin wannan shiri a wasu 'yan shekaru da suka gabata a wasu birane uku na kasar kuma ya yi babban tasiri, a wannan karon ana son fadada shirin zuwa ga sauran yankuna da suke da musulmi da dama a kasar ta Jamus.

Babbar manufar gudanar da wannan shiri dai ita ce samar da hanya ta tuntubar juna tsakanin dukkanin musulmi wadanda ba su fahimtar yaren wasu daga cikinsu, kamar Turkawa da larabawa.

661521

captcha