Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran wam na kasar hadaddiyar daular larabawa an bayyana cewa, An kammala gasar karatun kur'ani da harda da kuma hadisi ta kasashen larabawa na khalij tare da bayyana sunayen wadanda suka lashe gasar wadda a ka gudanar a birnin Dubai.
Wannan gasa dai tana daya daga cikin fitattun gasar kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a kowace shekara a cikin kasashen larabawa, tare da halartar makaranta da kuma mahardata kur'ani mai tsarki.
Wannan dai shi ne karo na 23 da aka gudanar da wannan gasa, kuma tuni aka sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar a dukkanin bangarorin da aka gudanar da ita.
661533