Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait an habarta cewa, an fara gudanar da wani zaman taro na kasa da kasa a kasar spain mai taken Musulunci da tattaunawar addinai a jami'ar sarkistah ta kasar ta Spain.
Jami'ar birnin sarqistah ce ta dauki nauyin shirya gudanar da wannan zaman taro da nufin karfafa mabiya addinai wajen gudanar da tattaunawa a tsakaninsu don samun fahimtar juna.
Wannan zaman taro ya hada mabiya addinai daban-daban musamman ma dai musulmi da kuma mabiya addinaina kiristanci da yahudanci.
661584