Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto da ke cewa za a fara gudanar da zaman taron ministocin kula da muhalli na kasashen musulmi a birnin Tunis na kasar Tunisia a cikin makon gobe idan Allah ya kaimu.
Zaman taron wanda hukumar kula da bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO ta dauki nauiyin shiryawa, zai yi dubi ne kan muhimman batutuwa da suka danganci harkar muhalli a cikin kasashen musulmi.
Rahoton ya ce wannan shi ne karo na hudu da za a gudanar da irin wannan zama na shekara-shekara, da zai samu halartar ministocin kula da muhalli daga kasashe saba'in da biyar.
661599