Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Iqtisadiyya an bayyana cewa, An buga tare da yada littafin Qods taswirar Musulunci ta hakika wanda cibiyar kula da harkokin rubutu ta kasar Syria ta dauyin bugawa da raba shi a cikin kasashen duniya daban-daban.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan littafin yana dauke da muhimman abubuwa da ya kamata musulmi da ma wadanda musulmi su dangane da matsayin Qods a addinin muslunci, da dalilan da suka sanya masallaci mai alfarma ya zama abin girmamawa a wajen musulmi.
Wannan cibiya da ked a dangantaka kai tsaye da ma'aikatar bunkasa harkokin ilimi da al'adu kasar Syria, ta gudanar da wannan babbar hidima ne da nufin wayar da kai kan karairayin yahudawa dangane da masallacin Qods.
661644