Bangaren kasa da kasa; An buga tare da yada littafin rayuwar iyali a mahangar addinin muslunci, tare da fatawoyi malaman fikuhun musulmi, bayan da malaman jamiar Azhar ta kasar suka yi dubi tare da tabbatar da shi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani labari daga shafin sadarwa na yanar gizo na muhit cewa, An buga tare da yada littafin rayuwar iyali a mahangar addinin muslunci, tare da fatawoyi malaman fikuhun musulmi, bayan da malaman jamiar Azhar ta kasar suka yi dubi tare da tabbatar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan littafi yana tattare da muhimman abubuwa da yakamata musulmi su sani da suka shafi rayuwar zamantakewar iyali, da kuma yadda Musulunci ya shiryata.
A cikin littafin akwai batun tarbiyar yara 'ya'ya maza da 'ya'ya mata da kuma yadda ya kamata a baiwa kowannensu tarbiya irin ta addini daidai koyarwar kur'ani.
661588