Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na Aljazeeranet an bayyana cewa, jami'ar Azhar da ke kasar Masar ta mayar da martani kan wani malamin addinin kirista da ya yi kira da a cire wasu ayoyi daga cikin kur'ani mai tsarki da ya ce sun saba wa akidar kiristanci kan yadda suke dauki Annabi Isa (AS)
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan malamin addinin kirista ya bayyana wasu daga cikin ayoyin kur'ani mai tsarki da cewa ba daidai suke ba, domin kur'ani ya yi daidai da akidarsu ya kamata cire irin wadannan ayoyi.
A nasa bangaren babban malamin Azhar kuma mai bayar da fatawa Sheikh Tayyib Ahmad ya mayar da martani kan wannan furuci, tare da jan kunnen malamin addinin kirista da ya yi hattara da abin da yake fada.
661828