Bangaren fikira da ilimi; Mataimakin shugaban kasar Iran kuma shugaban cibiyar bunkasa harkokin al'adu ta kasar Iran Mehdi Mostafavi, ya bayyana cewa fadada dangantaka tsakanin Iran da kuma Algeria na da matukar amfani ga duniya Musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada mataimakin shugaban kasar Iran kuma shugaban cibiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi ta kasar Iran Mehdi Mostafavi, ya bayyana cewa kara fadada dangantaka tsakanin jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma Algeria na da matukar amfani ga duniya Musulmi baki daya.
Ya ci gaba da cewa ko shakka babu matsayin dangantaka tsakanin wadannan muhimman kasashen Musulunci guda na girma, domin kuwa Algeria da Iran kasashe da suke taka gagarumar rawa a fagage da dama na harkokin Musulunci a duniya.
Iran da Algeria dai suna da daddiyar alaka da ta dauki lokaci ana bunkasa ta abangarori da dama na al'adu da ilimi, wanda hakan ke tabbatar da muhimmancin su a duniyar Musulunci.
662370