Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar rasid an bayyana cewa, za a wallafa wani littafi da zai kunshi mahangar babban malamin addinin nan na kasar Labanan marigayi Allah Fadlollah a bangarorin fikihun Musulunci a yankin Katif da a halin yanzu yake cikin kasar Saudiyya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai gudana ne a Husainiyar Almobarak da ke yankin, tare da halartar manyan malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) da ke yankin.
Yanzu haka dai an harhada da dama daga cikin littafan marigayin da suke magana kan batutuwa da mas'alolin fikihu, wadanda suke suke bayyana mahangarsa kan mas'aloli da dama.
661845