Bangaren al'adu da fasaha; Za a gudanar da wani babban taron kara wa juna sani na yanki da a kasa gudanarwa shekara-shekara wanda a wannan karon za a gudanar a kasar Tanzania a birnin Darussalam.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, banagraen watsa labaransa na gabacin nahiyar Afirka ya habarta cewa, Za a gudanar da wani babban taron kara wa juna sani na yanki da a kasa gudanarwa shekara-shekara wanda a wannan karon za a gudanar a kasar Tanzania a birnin Darussalam fadar mulkin kasar.
Wannan taro zai samu halartar malaman addini da jami'an gwamnati gami da fitattun masana da suka hada malaman jami'a daga kasashen yankin gabacin nahiyar Afirka da kuma kudancin nahiyar.
Kasashen kuwa sun hada da kasashen Muzambik, Rwanda, Brundi, Malawi, Zambia, Congo, Madagaska, Kenya, Uganda, Komoros da kuma Afirka ta kudu.
Babbar manufar gudanar da zaman taron dai ita ce kara wa juna sani kan muhimman lamurra da suka danganci hikimar aikin haji a addinin Musulunci.
661797