Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na media 73 an bayyana cewa, za a samar da wani shiri na musamman na wayar da kan matasa a kasar Switzerland dangane da addinin muslunci, karkashin bangaren nazarin ilimin tauhidi na jami'ar Losern da ke kasar.
Babbar manufar wannan shiri dai ita ce samar da wata hanya ta kara wayar da kan mutanen kasar Switzerland dangane da samun masaniya kan addinin muslunci, wanda hakan zai ba su damar yin bincike kansa.
Yanzu haka dai musulmin kasar Switzerland suna kokarin ganin cewa sun fadada ayyukansu na al'au da ilmantarwa, saboda karancin fahimtar addininsu a kasar.
662246