IQNA

An Buga Tare Da yada Littafin Kiran Sallah A Birnin Istanbul

10:24 - September 27, 2010
Lambar Labari: 2002117
Bangaren kasa da kasa, An buga tare da yada littafin kiran sallah a birnin Istanbul na kasar Turkiya, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin al'adu da ke birnin ta dauki nauyin bugawa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na jaridar zaman ta kasar Turkiya cewa, an buga tare da yada littafin kiran sallah a birnin Istanbul na kasar Turkiya, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin al'adu da ke birnin ta dauki nauyin bugawa tare da yadawa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan littafin ya tsokaci kan muhimmancin kiran sallah a cikin al'adun kasar Turkiya, a matsayinta na daya daga cikin kasashe masu dadden tarihin Musulunci.

Kasar Turkiya dai ta kasance kasa mai muhimmanci a cikin kasashen musulmi, wadda ta taka gagarumar rawa wajen yada akidu da koyarwa gami da al'adun Musulunci a sassa na duniya.

662763



captcha