IQNA

Cibiyar Bincike Ta Azhar Ta Jaddada Wajabcin Girmama Addinai

10:24 - September 27, 2010
Lambar Labari: 2002122
Bangaren kasa da kasa; Babbar cibiyar bincike da nazari ta Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ta jaddada wajabcin girmama juna tsakanin dukkanin mabiya addinai na duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na babban malamin jami'ar Azhar kuma mai bayar da fatawa na jami'ar Sheikh Ahmad Tayyib cewa, cibiyar bincike da nazari ta Azhar na jaddada wajabcin girmama juna tsakanin dukkanin mabiya addinai na duniya baki daya.

Shehin malamin ya bayyana hakan ne a cikin bayanin day a fitar da sunan jami'ar a matsayinsa na bababn malami a cikinta, inda ya bayyana cewa babu dalilin da zai sanya wasu mabiya wani addini su yi dirar mikiya kan wani addini.

Bayanin na sheikh Ahmad Tayyb ya z one a daidai lokacin da ake ci gaba da yin dirar mikiya kan addinin Musulunci daga sassa daban-daban na kasashen duniya musamman ma a nahiyar turai.

662806



captcha