IQNA

Jawaban Shugaban Iran A New York Sun Dimautar Da Makiya

10:23 - September 27, 2010
Lambar Labari: 2002129
Bangaren siyasa, Ayatollah Ozma Nuri Hamedani yabbayana jawaban da shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad ya gabatar a babban zauren majalisar dinkin duniya da ke birnin New York da cewa sun dimauta makiya.



Kamfanin dilllancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren sadar na ofishin daya daga cikin malaman addinin muslunci da ke birnin Qom cewa, Ayatollah Ozma Nuri Hamedani yabbayana jawaban da shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad ya gabatar a babban zauren majalisar dinkin duniya da ke birnin New York da cewa sun dimauta makiya tare da kunyata su.

Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin ya gana da wasu daga cikin manyan kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran a babban ofishinsa da ke birnin na Qom, inda ya jaddada wajabcin yin tsayin daka a gaban makiya, tare da nuna jaruntaka.

Ya ce ko shakka babu babbar jaruntaka da shugaba Mahmud Ahamdinejad ya nuna taron majalisar dinkin duniya, abin burgewa ne kuma daukaka ce ga dukkanin musulmi da 'yantattu a duniya.

663312







captcha