IQNA

Ministocin Harkokin Wajen Musulmi Sun Soki Siyasar Isra'ila

10:23 - September 27, 2010
Lambar Labari: 2002131
Bangaren kasa da kasa; Ministocin harkokin wajen kasashen musulmi sun yi kakkausar suka dangane da siyasar zalunci da danniya gami da maya ta haramtacciyar kasar Isra'ila.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ministocin harkokin wajen kasashen musulmi sun yi kakkausar suka dangane da siyasar zalunci da danniya gami da maya ta haramtacciyar kasar Isra'ila a zaman da suka gudanar a birnin New York na kasar Amurka.

Bayan kammala zaman da ministocin harkokin wajen kasashen musulmin suka gudanar a gefen zaman taron babban zauren majalisar dinkin duniya, sun fitar da bayani na bai daya, da ke yin Allawadai da siyasar mamaya ta Isra'ila.

Bayanin ya ce haramtacciyar kasar Isra'ila ta tabbatar da cewa ba a shirye take ta komawa zuwa ga tattaunawar zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ba.

663187




captcha