Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zaman taro a matsayi na kasa da kasa a birnin Makka mai alfarma, dangane da harkokin tattalin arziki na muslunci, wanda jami'ar ummul qura ta dauki nauyin shiryawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arabic.business.maktoob an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro a matsayi na kasa da kasa a birnin Makka mai alfarma, dangane da harkokin tattalin arziki na muslunci, wanda jami'ar ummul qura ta dauki nauyin shiryawa tare da gudanarwa.
Daga cikin abubuwa da za a gudanar a wannan zaman taro, har da gabatar da jawabai kan kusanto da fahimtar juna tsakanin masana harkokin tattalin arziki na kasashen duniya, da kuma takwarorinsu masana na kasashen musulmi.
An shirya gudanar da zaman taron ne tare da hadin gwiwa tsakanin jami'ar ummul qura da kuma ma'aikatun bunkasa harkokin tattalin arziki da yawun shakatawa na kasar Saudiyya.
663897