Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran muhit an bayyana cewa, majami'ion kasar Masar sun mayar da martani kan malamin kiristan kasar day a soki addinin muslunci ta hanyar bayyana kur'ani mai tsarki a matsayin littafi mai nakasu ta hanyar kara wasu ayoyi.
Bayanin bababn malamin addinin kirista na kasar Masar day a fitar, ya nuna barranta daga wannan furuci, da kuma bayar da hakuri ga dukkanin musulmin kasar, tare da yin kira zuwa ga zaman lafiya da fahimta gami da girmama juna.
Babban sakataren kungiyar majami'oin kasar Masar ya yi furucin da ya bakantawa musulmi a dukkanin fadin kasar ta Masar da kuma kasashen larabawa gami da kasashen musulmi.
663679