Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na lablover na yanar gizo cewa a saka wani kur'ani dadadde a kasuwa a birnin London na kasar Birtaniya, wanda lokacin rubutunsa ke komawa zuwa ga zamanin halifancin Amirul muminin Ali (AS) wato kimanin shekaru sama da dubu daya da dari uku da 'yan kai.
Wannan kur'ani na daya daga cikin muhimman kayayykin tarihin muslunci da ke ajiye a kasar Birtaniya, wanda yanzu haka aka yi wa kimar kudi har dala dubu dari biyu da talatin da bakwai.
An kai wannan kur'ani a kasar Birtaniya net un sama da shekaru 50 da suka gabata, kuma ana ci gaba da adana shi a wani babban dakin kayan tarihi na kasar.
663640