IQNA

Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Kasar Kuwait

16:24 - September 28, 2010
Lambar Labari: 2003334
Bangaren kasa da kasa; Ana ci gaba da gudanar da gasar karatu kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait, inda matasa makaranta daga sassa daban-daban na kasar suke ci gaba da kara wad a juna.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar kasar Kuwait ta Al'anba ta buga labarin cewa cewa Ana ci gaba da gudanar da gasar karatu kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait, inda matasa makaranta daga sassa daban-daban na kasar suke ci gaba da kara wa da juna a gasar.

Wannan gasar kur'ani ana gudanar da ita ne a karo na goma sha shida, a yankin Almubarak na kasar, daga cikin alkalan da suke sanya a ido kan yadda gasar take gudana akwai maza biya da kuma mata.

Gasar tana samun halart makaranta mata da maza dukkanin matasa na kasar, bayan kammala mataki na karshe za a bayar da kyautuka ga wadanda suka zo na daya da na biyu da na uku.

663602



captcha