Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da jaridar kasar Masar ta yaum sabi ta buga an bayyana cewa, babban jagoran majami'ar kibtawa a kasar Masar ya nemi uzuri daga mabiya addinin muslunci na kasar kan cin zarafin da babban sakataren majami'oin kasar ya yi a cikin makon da ya gabata a kasar.
Jagoran majami'r Kibtawan ya bayyana neman uzurin nasa a cikin wata zantawa da ta hada shi da tashar talabijin din kasar, inda ya ce hakika ya yi bakin cikin jin furucin da ya fito daga bakin babban sakataren majami'oin.
Ya ce yana kiran dukkanin musulmi da su yi hakuri, kuma su san cewa abin ya wancan mutumin ya fada ra'ayinsa ne, kuma ba yana wakiltar kiristoci ba ne da furucin nasa.
663555