Bangaren a'adu da fasaha; An fara gudanar da wani yin bahasi kan harkoki na kiyaye muhalli a mahangar addinin muslunci a Aman fadar mulkin kasar Jordan, wanda cibiyar Alil bait da ke kasar ta shirya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Al-rayi an bayyana cewa, an fara gudanar da wani yin bahasi kan harkoki na kiyaye muhalli a mahangar addinin muslunci a Aman fadar mulkin kasar Jordan, wanda cibiyar Alil bait da ke kasar ta shirya gudanarwa.
Wannan cibiya wadda tana daya daga cikin cibiyoyin da kan shirya taruka da suka danganci addini a kasar ta Jordan tan akarkashin kulawar sarkin kasar ne Abdllah na biyu, wanda yake jagorantar taron.
Zaman taron dai na samun halartar masana daga sassa sassa daban-dana na kasar, inda ake gabatar da laccoci kan matsayin tsaftar muhalli a mahangar muslunci.
663822