Bangaren kasa da kasa; majami'ar Apostholic ta Armaniyawa ta yi kakkausar suka dangane da cin zarafin musulmi da ake yi ta hanyar keta alfarmar kur'ani, tare da yin Allawadai da duk wani yunkuri na tozarta wani addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na news cewa, majami'ar Apostholic ta Armaniyawa ta yi kakkausar suka dangane da cin zarafin musulmi da ake yi ta hanyar keta alfarmar kur'ani, tare da yin Allawadai da duk wani yunkuri na tozarta wani addini a duniya.
Majami'ar ta sanar da hakan ne a cikin wani bayani da ta fitar, wanda kafofin yada labarai suka dauka, inda ta tabbatar da cewa rayuwa tsakanin al'ummomin duniya na bukatar girmama juna da akidoji gami da addinai na dukkanin al'ummomi.
Haka nan kuma majami'ar ta kirayi dukkanin jagororin addinai da suka karfafa tattaunawar addinai da nufin kara samun fahimtar juna tsakanin mabiya addinai.
664608