Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran Bernama cewa, fira ministan kasar Malazia Mashita Ibrahim ya bayyana cewa yin wulakanci ga addinin muslunci baa bin yafewa ba ne, dole a dauki dukkanin matakai na shiga kafar wando daya da masu yin wannan mummunan aiki.
Bayanin ya ci gaba da cewa, a cikin wani bayani da ya gabatar fira ministan kasar ta Malazia ya jaddada wajabcin daukar dukkanin matakan da suka dace domin ladabtar da duk masu yin hawan kawara kan akidun muslunci.
Furucin na fira ministan Malazia ya zo a daidai lokacin da ake ta magana kan cin zarafin da musulmi suke fiskanta daga wasu daga mutanen nahiyar turai da Amurka, tare da keta alfarmar ababe masu tsarki a Musulunci.
664473