Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani zaman taro a matsayi na kasa da kasa a birnin Izmir na kasar Turkiya, da ke yin bahasi kan yanayin abinci a kasashen musulmi ta fuskar wadatarsa ko karancinsa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, An fara gudanar da wani zaman taro a matsayi na kasa da kasa a birnin Izmir na kasar Turkiya, da ke yin bahasi kan yanayin abinci a kasashen musulmi ta fuskar wadatarsa ko karancinsa.
Wannan zaman taro da ke samun halartar wakilai daga gwamnatocin kasashen musulmi da kuma kungiyoyin kula da harkokin abinci a kasashen musulmi, yana yin dubi a kan hanyoyin taimakon juna kuma alokaci guda tsakanin dukakncin kasashen.
Daga cikin kasashen musulmi dai akwai kasashen da suke fuskantar matsalolin abinci sakamakon fari da aka samu a yankunansu a cikin wannan shekara, inda taron bai manta da su ba.
664578