Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na risalehaber cewa, za a gudanar da wani zaman taro na kungiyoyin fararen hula na kasashen musulmi a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya a cikin mako mai zuwa.
Baynin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro kwamitin kungiyoyin farar hula na kasashen musulmi ne ya dauki nauyin shirya shi da kuma gudanar da shi a kasar turkiya, karkashin jagorancin Najmi Sadiq Auglo.
Daga cikin muhimman abubuwan da taron zai mayar da hankali kansu akwai batun ambaliyar ruwan da afku a kasar Pakistan, tare da yin sanadiyar lakume rayukan dubban mutane, gami da batun killace Gaza.
665290