IQNA

Taron Kusanto Da Mazhabobin Musulunci A Birnin London

12:16 - September 30, 2010
Lambar Labari: 2004444
Bangaren kasa da kasa; A ranar Asabar mai zuwa za a fara gudanar da zaman taro na kasa da kasa na kusanto da mazhabobin mulunci a karo na hudu, wanda za a gudanar a birnin London.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ranar Asabar mai zuwa za a fara gudanar da zaman taro na kasa da kasa na kusanto da mazhabobin mulunci a karo na hudu, wanda za a gudanar a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai samu halartar manyan malamai da masana musulmi daga sassa daban-daban na kasashen duniya, kuma za a gudanar da zaman taron a babban dakin taruka na cibiyar Musulunci da ke birnin.

Daga cikin muhimman abubuwan da taron zai mayar da hankali kansu akwai batun hadin kan musulmi da kusanto mazhabobinsu, wanda hakan shi ne bababn dalilin kafa wannan wannan cibiya.

665342





captcha