Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa an bayyana cewa, wakilin musulmi na farko a majalisar dokokin kasar Australia ya yi rantsuwar fara aiki da kur'ani mai tsarki a gaban majalisar kasar ta Australia.
Bayanin ya ci gaba da cewa Edhusich wanda mahaifansa musulmin kasar Bosnia ne da suka hijira zuwa kasar Australia, shi ne ya tsaya takarar neman shugabancin majalisar dokokin kasar a matsayin wakilin musulmin kasar a majalisa.
An zabe shi ne a matsayin wakilin musulmi wadanda su ne kashi biyu cikin dari na mutanen kasar Australia, wadanda suka cancanci wakili a majalisar.
665367