Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kungiyar gwagwarmaya ta jihadul islami an bayyana cewa Qods bridgates reshen soji na kungiyar jihadul islami ya yi kira zuwa wani sabon bore ga mamamya da zaluncin yahudawan sahyuniya kan al'ummar palastinu a daukacin yankunan palastine.
Ya zo a cikin bayanin cewa sama da mambobin dakarun da shugabanninsu 654 ne suka yi shahada sakamakon hare-haren ta'addancin haramtacciyar kasar Isra'ila a kan al'ummar palastinawa.
Wannan adadi na wadanda suka yi shahada da cikin dakarun daga cikin shekara ta 2000 ne da aka fara intifada ta biyu zuwannan lokaci.
665380