Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran wanm na kasar hadaddiyar daular larabawa an bayyana cewa, kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta yi Alladawai tare da yin kakakusar suka dangane da yada littafin zarafi da keta alfarmar ma'aikin Allah (SAW) ta hanyar zanen batunci.
Babban sakataren kungiyar ne Ikmal Ihsan Auglu ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya bayyana cewa yada zanen batuncin da aka yi ga manzon Allah (SAW) ya harzuka musulmi a ko'ina suke cikin fadin duniya.
An fitar da wannan bayanin ne da nufin mayar da martani kan matakin da aka dauka na yada littafin nan na cin zarafi da zanen batuncin ga manzo da aka yi a kasar Danmark.
666499