Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran saba na kasar Yeman an habarta cewa, an gudanar da wani taron girmama mahardata kur'ani mai tsarki 132 da suka kammala samun horo na hardar kur'ani mai tsarki a kwalejin kur'ani mai tsarki da ke birnin San'a a kasar.
A wajen gudanar da wannan taro, an gabatar da jawabai na jinjinawa ga dukkanin daliban da suka kammala samun wannan horo, tare da jan hankalinsu zuwa ga koyarwar addini da riko da dabi'un Musulunci.
Babbar manufar gudanar da wannan shiri na hardar kur'ani mai tsarki ita ce kwadaitar da matasa zuwa ga karatun kur'ani, da kuma koyon abubuwan da yake koyarwa na sanin addini da shari'a.
666553