IQNA

Makaranta Kur'ani Daga Karbala Sun Kai Ziyara A Qom

15:09 - October 02, 2010
Lambar Labari: 2005518
Bangaren kasa da kasa; Wata tawagar makaranta kur'ani mai tsarki daga birnin Karbala mai alfarma ta kawo wata ziyara a birnin Qom mai alfarma, domin agnewa idanunsu wurare masu tsarki da ke birnin.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ruqayah.net cewa, wata tawagar makaranta kur'ani mai tsarki daga birnin Karbala mai alfarma ta kawo wata ziyara a birnin Qom mai alfarma, domin agnewa idanunsu wurare masu tsarki da ke birnin na Qom.

Tawagar dai ta kunshi wasu daga fitattun makaranta kur'ani mai tsarki na kasar Iraki, kamar su Musatafa Sarraf makarancin na kasa da kasa dan kasar Iraki, inda suka kai ziyara zuwa cibiyoyin kur'ani da ke cikin wannan gari.

Dukkanin wadanda suke cikin wannan tawaga dai dalibai da kuma mambobi a cibiyar kur'ani mai tsarki ta ruqayya da ke birnin Karbala mai alfarma.

666515



captcha