IQNA

Za A Girmama Mahardata Kur'ani Mai Tsarki Dubu 13 A Gaza

15:09 - October 02, 2010
Lambar Labari: 2005522
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da bikin girmamam mahardata kur'ani mai tsarki dubu 13 a garin Gaza, bayan da suka kammala samun horon harda a karashin wani shiri na ma'aikatar kula da harkokin al'adu.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga daga shafin sadarwa na jaridar kasar Masar yaum sabi an habarta cewa, za a gudanar da bikin girmamam mahardata kur'ani mai tsarki dubu 13 a garin Gaza, bayan da suka kammala samun horon harda a karashin wani shiri na ma'aikatar kula da harkokin al'adu ta yankin.

Abu Talib Abu shir ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta gwamnatin Gaza ya bayyana cewa, dukknain daliban da suka samu wannan horo na hardar kur'ani sun fara gudanar da hardar a cikin wannan bazarar.

Ya kara da cewa wannan shirin na daya daga cikin shirye-shiryen da suka samu nasara, kuma fira ministan yankin Isma'ila Haniyya zai samu halartar taron girmama mahardatan.

666581



captcha