Bangaren kasa da kasa; Cibiyar kur'ani mai tsarki ta Baitul kur'an da ta kebancin gudanar da ayyuka gami da harkokin kur'ani na mata a birnin Saihat na kasar Saudiyya, za ta fara aiwatar da wani shiri na kur'ani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran muzn an habarta cewa, cibiyar kur'ani mai tsarki ta Baitul kur'an da ta kebancin gudanar da ayyuka gami da harkokin kur'ani na mata a birnin Saihat na kasar Saudiyya, za ta fara aiwatar da wani shiri na kur'ani mai tsarki.
Wannan shiri zai kunshi wasu daga karatuka na fikihun kur'ani da kuma tafsirin wasu daga cikin ayoyin kur'ani mai tsarki gajeru, gami da koyon tajwidi, wait ilimin sanin ka'idoin karatun kur'ani.
Haka nan kuma wannan shirin zai hada koyar da kanan yara karatun kur'ani mai tsarki tare da sanin tarjamar wasu daga cikin ayoyi, wanda zai kwashe tsawon watanni uku ana gudanar da shi.
666614