IQNA

Za A Gudanar Da Tarukan Shahadar Imam Sadiq (AS) A Saudiyya

12:41 - October 03, 2010
Lambar Labari: 2005895
Bangaren kasa da kasa; Mabiya mazhabar iayalan gidan manzon Allah (SAW) a yankin Shrkiyya na kasar Saudiyya suna shirin gudanar da tarukan ta'aziyyar shahadar Imam Sadiq (AS)



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga tashar sadarwa ta rasid an bayyana cewa, mabiya mazhabar iayalan gidan manzon Allah (SAW) a yankin Shrkiyya na kasar Saudiyya suna shirin gudanar da tarukan ta'aziyyar shahadar Imam Sadiq (AS) a yankunansu.

A lokacin da zaman taron da za a yi gobe idan Allah ya kaimu, hard a jawabai kan matsayin Imam Sadiq (AS) da kuma sauran limaman iyalan gidan manzon Allah (SAW) daga cikin malaman da za su gudanar da jawabi har da Naji Ibadi.

Wakilan cibiyoyin muslunci musamman ma na mabiya tafarkin iayalan gidan manzon Allah (SAW) za su halarci taron, kamar yadda kuma Said Mu'atik shi ma zai gabatar da jawabi.

667241


captcha