IQNA

Mahardata 8 na Burnai Na Halartar Gasar Kur'ani A Indonesia

12:41 - October 03, 2010
Lambar Labari: 2005899
Bangaren kasa da kasa; Takwas daga cikin mahardata kur'ani daga tsibirin Burnai ne su ke halartar gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a Indonesia.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habrta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadara na yanar gizo na Bru Direct cewa, takwas daga cikin mahardata kur'ani daga tsibirin Burnai ne su ke halartar gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Jakarta.

Dukkanin masu halartar wannan gasa dai an kasa zuwa kashi hudu ne, daga ciki hard a masu hardar dukkanin kur'ani mai tsarki, sai kuma masu hardar rabinsa, da kuma masu hardar kashi daya bisa hudu.

Daga cikin kasashen da suke halartar wannan gasa dai ban da kashen gabacin Asia, akwai kasshen tsakiyar Asia da kuma kudancin nahiyar kamar Pakistan da kuma tsibirin Burnai.

667097



captcha