IQNA

Imam Hussain (AS) Ramzi Ne na Kare Hakkin Biladama

16:03 - October 03, 2010
Lambar Labari: 2006019
Bangaren kasa da kasa, Babban limamamin masallacin Najaf Ashraf Sayyid Sadruddin Kubanci ya bayyana cewa, Imam Hussain (AS) ya sadaukantar da rayuwarsa mai albarka domin kare hakkin bil adama da tabbatar adalci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na alqubanchi an bayyana cewa, babban limamamin masallacin Najaf Ashraf Sayyid Sadruddin Kubanci ya bayyana cewa, Imam Hussain (AS) ya sadaukantar da rayuwarsa mai albarka domin kare hakkin bil adama da tabbatar adalci a bayan kasa.

Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan wasu masu sukar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) da suke gudanar da tarukan Ashura, da tunawa da shahadar Imam Hussain (AS) da suke bayyana hakan da cewa babban koma baya ne a cikin addini.

Kubanci ya ce raya tarukan Ashura shi ne babban ci gaba da wayewa, domin kuwa raya tunanin Ashura raya tunanin hakianin koyarwar manzon Allah ne, ta kare hakkin dan adam da karamarsa da akidarsa da makomarsa.

667036



captcha