IQNA

Taron Cibiyar Kusanto Da Mazhabobi Kai Tsaye A Yanar Gizo

16:02 - October 03, 2010
Lambar Labari: 2006020
Bangaren kasa da kasa; Cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci za ta gudanar da bababn taronta na kasa da kasa a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda za a watsa kai tsaye a shafin cibiyar na yanar gizo.



Kamfanin dillancin labaran qina ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na cibiyar muslunci ta birnin London cewa, cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci za ta gudanar da bababn taronta na kasa da kasa a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda za a watsa kai tsaye a shafin cibiyar na yanar gizo na wannan cibiya.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daga cikin irin tarukan da wannan cibiya ke gudanarwa da nufin hada kan musulmi da dukkanin mazhabobinsu, inda wasu lokuta a kan gudanar da tarukan a cikin kasashen musulmi, wasu lokutan kuma a cikin kasashen yamma.

Yanzu haka dai wasu daga cikin mambobin cibiyar da ke wakiltarta a wasu kasashen musulmi sun fara isa birnin London domin fara gudanar shirye-shiryen taron.

666977



captcha