IQNA

An Bude Wani Ofishi Na Masana Mata A Birnin Tehran

16:02 - October 03, 2010
Lambar Labari: 2006022
Bangaren kasa da kasa, An bude wani ofishi na masana musulmi mata a birnin Tehran karkashin inuwar cibiyar bunkasa harkokin ilmi da al'adu ta kasashen muslmi ISESCO tare da halartar mataimakin babban sakataren cibiyar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar ISESCO an bayyana cewa, an bude wani ofishi na masana musulmi mata a birnin Tehran karkashin inuwar cibiyar bunkasa harkokin ilmi da al'adu ta kasashen muslmi ISESCO tare da halartar mataimakin babban sakataren cibiyar Hadi aziz.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan ofishi zai mayar da hankali wajen yin amfani da wannan damanr domin samun fahimta tsakanin dukkanin masana mata muslmi a dukkanin kasashen musulmi, ta yadda za su iya yin aiki kafada da kafada domin ci gaban addinin muslunci.

Yanzu haka dai wasu daga cikin fitattun mata musulmi masa sun nuna sha'awarsu wajen ganin sun bayar da gudunmuwarsu a wannan ofishi.

666931



captcha