IQNA

An Kammala Gasar Kur'ani Ta Jami'an Tsaro A Kuwait

16:02 - October 03, 2010
Lambar Labari: 2006023
Bangaren kasa da kasa, An kamamla gasar karatun kur'ani mai tsarki ta jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da sojoji a kasar Kuwait, da nufin kara karfafa gwiwarsu wajen harkokin kur'ani mai tsarki.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habrta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Al-ra'y ta kasar Kuwait an habarta cewa, an kamamla gasar karatun kur'ani mai tsarki ta jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da sojoji a kasar Kuwait, da nufin kara karfafa gwiwarsu wajen harkokin kur'ani.

Ma'iakatar kula da harkokin addini t akasar tare da hadin gwiwa da cibiyar bunkasa ayyukan kur'ani a kasar ne kan shirya gudanar da irin wannan gasar kur'ani mai tsarki da ta kebancin jami'an tsaro kawai.

Babbar manufar gudanar da gasar dai ita ce kara jami'an tsaron karfin gwiwa wajen yin amfani da koyarwar kur'ani a cikin dukkanin ayyukansu, musamamn ma dai da ayyukan da suka shafi rayuwarsu.

666857










captcha