IQNA

An Kammala Gasar Karatun Kur'ani Mai Tsarki A Iraki

16:02 - October 03, 2010
Lambar Labari: 2006024
Bangaren kasa da kasa; An kammala gasar karatun kur'ani mai tsarki a garin Babul da ke cikin kasar Iraki, da ta samu halartar malamai da makaranta daga sassan kasar.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalyo daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kur'ani na Muzn cewa, an kammala gasar karatun kur'ani mai tsarki a garin Babul da ke cikin kasar Iraki, da ta samu halartar malamai da makaranta daga sassan kasar baki daya.

Rahoton ya ci gaba da cewa babban abin da gasar ta mayar da hankali a kansa shi ne ilimi tajwidi da kiyaye shi a cikin dukkanin karatun da aka gabatar a cikin gasar, gami da la'akari da fitar da haruffan kamar yadda suke.

Bayan kammala gasar wadda cibiyar shahid Mihrab ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, an bayar da kyautuka na musamamn ga dukaknin wadanda suka lashe gasar.

666794



captcha