Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa hqmi.org.sa an bayyana cewa, an gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki a kasar Brundi tare da halartar mahardata da makaranta kur'ani mai tsarki daga sassa daban-daban na gabacin nahiyar Afirka da kewaye.
Babban kwamitin kula da shirya harkokin gasar kur'ani mai tsarki na duniya ya shirya gudanar da wannan gasa, inda kimanin makaranta 50 suke halartar gasar tare da alkalai na kasa da kasa.
Yanzu haka dai kwamitin yana da shirin shirya wasu gasa-gasa na kur'ani a wasu kasashen da ke gabacin nahiyar nahiyar Afirka da nufin kara fadada koyarwar kur'ani mai tsarki a cikin nahiyar.
668295