IQNA

Za A Gudanar Da Shirin Horar Da Mata A Cibiyoyin Kur'ani Na Qatar

21:17 - October 05, 2010
Lambar Labari: 2007275
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani shiri na horar da mata a cibiyoyin kur'ani mai tsarki na kasar Qatar, ya yadda za a iya samun mata masu kwarewa wajen tafiyar da cibiyoyin addini da na kur'ani a kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Al-raya ta kasar Qatar an bayyana cewa, za a gudanar da wani shiri na horar da mata a cibiyoyin kur'ani mai tsarki na kasar Qatar, ya yadda za a iya samun mata masu kwarewa wajen tafiyar da cibiyoyin addini da na kur'ani a kasar ta Qatar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri za a fara aiwatar da shi ne a cikin makonni biyu masu zuwa, tare da hadin gwiwa da jami'ar Musulunci ta kasashen turai, da nufin kara bayar da dama ga mata su taka rawa ta wannan fuska.

Daga cikin muhimman abubuwan da shirin zai mayar da hankali kansu akwai batun samar da mata goggagu ta bangaren kur'ani mai tsarki da sauran ilmomi na addini.

668275




captcha