Kamfanin dilalncin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar muslunci da ke kasar Birtaniya an bayyana cewa, An karanta bayanin bayan taron kusanto da mazhabobin muslunci da aka gudanar a birnin London an kasar Birtaniya a cikin wannan mako.
Wannan dai karo na hudu da aka gudanar da wannan zaman taro na shekara-shekara da kwamitin ke gudanarwa, taron da ya samu halartar masana da malamai daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da na larabawa.
Babbar manufar gudanar da zaman taron dai ita ce yin bita kan muhimman abubuwa da zaman taron ya tattauna a kansu a zaman na shekarar da ta gabata, da kuma kara daukar matakan hada kan musulmi.
668218