IQNA

Fatawar Jagora Ta Samu karbuwa A Duniyar Musulmi

21:30 - October 05, 2010
Lambar Labari: 2007287
Bangaren kasa da kasa; Fatawar jagoran juyin juya halin muslunci kan haramta yin batunci ga matan manzon Allah (SAW) da fitattun 'yan sunna ta samu karbuwa a tsakanin al'ummomin musulmi na duniya.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na muhit an bayyana cewa, Fatawar jagoran juyin juya halin muslunci kan haramta yin batunci ga matan manzon Allah (SAW) da fitattun 'yan sunna ta samu karbuwa a tsakanin al'ummomin musulmi na duniya baki daya.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan fatawa wadda nuna matsayin malaman shi'a dangane da matsayin matan manzon Allah da kuma fitattun malaman sunna a wajen shi'a, ta tabbatar da cewa malaman shi'a ba su da wata matsala da sunna, kumasuna neman zaman lafiya da hadin kan al'ummar musulmi ne.

Babban malami mai bayar da fatawa a jami'ar Azhar da ke kasar Masar Dr. Ahmad Tayyib ya yaba da wannan fatawa, ya kuma yi jinjina ga jagoran juyin juyin juya halin muslunci, inda ya bayyana cewa wannan fatawa ta nuna a fili cewa masu son tayar da fitina ba su wakiltar shi'a ko sunna.

668172
captcha